/A yayin da ake kulla alaka ta soyayya tsakanin mata da maza a koda wane lokaci, hakazalika aure wanda shine ribar kowace soyayya yana kasancewa idan alaka tayi karfi. A wannan makon Legit.ng ta kawo muku wasu sirrika musamman ga mata wajen rike miji a gidan aure da sai dai mutu ka raba idan ta kiyaye.
Ga jerin sirrikan kamar haka: 1. Tsafta: Tsafta tana daya daga cikin ababen da ya kamata kowace matar aure ta kiyaye domin ta kara neman tushen zama a zuciyar mijinta. 2. Girmamawa tare da mutuntuwa: Ya kamata kowace matar aure ta girmama mijin ta, iyayen sa, abokan sa, da kuma dangin sa baki daya. Hakan zai kara dankon soyayya tsakanin ta da mijin ta.
3. Sirri: Sirri yana daya daga cikin shikakai na aure, domin kuwa yana daya daga cikin ababe da ya kamata uwargida ta kiyaye wajen rufe asirin mai gidan ta ba tare da bayyana shi koda ga iyayen ta ba. 4. Hakuri: Ginshikin kowane al'amari na rayuwa yana bayuwa ne ga hakuri, domin har ta ibadun da muke sai mun yi hakuri da juriya zamu iya dabbaka su. Hakazalika ana son mace ta kasance mai hakuri fiye da mijinta a yayin da take dakin mijin ta. 5. Gaskiya da rikon amana: Wannan wani babban jigo ne da ya kamata matan aure su kiyaye, domin cin ribar zama a gidajen mazajen su.